Fitacciyar 'yar gwagwarmaya, Naja'atu Bala Muhammad ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da take hakkin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ta hanyar amfani da shari'a.
Da take magana a wata hira da DCL Hausa, Naja'atu ta ce akwai wasu mutane da ake zargi da aikata laifuffuka amma ba a ɗauki irin matakan da ake ɗauka kan El-Rufai a kansu ba, saboda suna da alaƙa da jam'iyyar APC mai mulki.
Ta kuma zargi gwamnati da aiwatar da doka bisa son rai, tana mai cewa ana yi wa El-Rufai wannan mataki ne saboda alaƙarsa da jam'iyyar African Democratic Congress (ADC).
Naja'atu ta ƙara da cewa ana yi wa tsohon gwamnan barazana tare da nuna masa rashin adalci, tana mai jaddada cewa matakan da ake ɗauka a kansa sun saba wa haƙƙoƙinsa na asali.
Comments
Add a comment