On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Najeriya Da Angola Sunki Amincewa Da Bukatar Kungiyar OPEC Na Rage Yawan Man Da Suke Hakowa

Najeriya da Angola sun ki amincewa da matakin da kungiyar kasashe masu arzikin fitar da man fetur ta duniya Opec ta bukaci su dauka, na rage yawan man da suke hakowa.

Rahotonni sun bayyana cewa, kawancen Kasashen da Saudiyya ke jagoranta ba su samu cimma matsaya ba da Angola da Najeriya, wadanda suka nuna  rashin amincewarsu  da  rage yawan man da suke  hakowa.

Wani wakili a yayin ganawar  ya ce ba lallai ba ne a iya cimma matsaya a tsakanin bangarorin biyu kafin taron da  kungiyar ta OPEC da  za’a yi  a  gobe  30 ga Nuwambar 2023.