On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Najeriya Ta Amfana Saboda Tafiye-Tafiyen Buhari Zuwa Ketare Inji Fadar Shugaban Kasa

shugaban Kasa Buhari

Gwamnatin taraiyya ta ce balaguron da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi zuwa kasashen waje, ta kawo ma kasar nan cigaba da dama, ta bangaren cigaban tattalin arzikin kasa.

Ministan Kasashen Waje , Geoffrey Onyema ne ya baiyana haka yau a Abuja  a  lokacin da yake gabatar da irin nasarorin da ma’aikatarsa  ta samu, a karkashin gwamnati mai ci.

Onyema ya  ce  balaguron da shugaban  kasar  yay i zuwa kasashen waje, inda ya gana da shugabannin kasashen  bata tsaya  ga iya  jawo hankalin masu  zuba jari zuwa kasar nan kadai ba, harma da daga  martabar da Najeriya ke dashi.

Ya kara da cewa, gwamnatin taraiyya ta karkashin ma’aikatarsa ta samar da shirye-shirye da dama wadanda  suka temaka  wajen kare  rayuwar  ‘yan Najeriya dake  zaune a kasashen waje.