On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Najeriya Ta Kai Wasan Karshe A Gasar WAFU Ta 'Yan Kasa Da Shekara 17

GOLDEN EGLEATES

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasa Yan Kasa da shekaru 17 Golden Eaglets zata kece raini da Kungiyar Kwallon Kafa ta Burkina Faso a wasan Karshe na Gasar cin Kofin Matasa Yan Kasa da Shekara 17 ta nahiyar Afrika ta shekarar Bana, wanda za’a yi a Cape Coast na kasar Ghana a ranar Juma’a.

A wasan Kusa dana karshe  na gasar da aka yi ranar Talata, Kungiyar Kwallon Kafa ta Burkin Faso ta Lallasa Mai Masaukin Baki Ghana da Ci 1 tak mai ban haushi , A yayin da Najeriya ta doke  kasar Cote d Ivoire  da  ci 3  da 1.

Sakamakon Wasan na biyu da aka yi jiya, Ya nuna cewa, Burkin Faso da kuma Kungiyar Kwallon kafa ta Golden Eaglets ne  zasu kasance a  gasar cin kofin kafa ta yan kasa da shekara 17  ta shekara mai zuwa  wadda  kasar Algeriya zata karbi Bakunci.

More from Labarai