On Air Now

ZANGON MARAICEN LAHADI

6:00pm - Midnight

Najeriya Ta Yi Kuskuren Kin Zaben Osinbajo A Matsayin Shugaban Kasa

Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi na biyu, ya ce Najeriya ta rasa samun damammaki da dama saboda rashin zaben mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a matsayin shugaban taraiyyar kasar nan.

Tsohon sarkin ya baiyana haka ne a yayin kaddamar da wani littafi  wanda aka  wallafa  kan mataimakin shugaban kasar a  jiya.

A cewarsa, Gazawar tsarin siyasa wajen marawa Osinbajo baya a matsayin shugaban kasa ya sa Najeriya ta kara samun kanta  cikin yanayi  na  tabarbarewa.

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya,Ya  baiyana  cewar  yana  day akin  cewa Osinbajo na daya daga cikin wadanda ke cikin gwamnati mai ci, da ke da ra'ayin yin muhawara a kan ko wane irin lamari da kuma bayar da hujja mai  inganci  kan yadda  za’a samu cigaban kasa.