On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Najeriya Zata Ciwo Bashin Tiriliyan 12 A Shekara Mai Zuwa

SHUGABAN KASA DA MINISTAR KUDI

Majalisar dattawa ta karkashin kwamitinta mai sanya ido kan baitul malin gwamnati, Ya nuna rashin amincewarsa da Ministar kudi ta kasa Zainb Ahmed, dangane da Daftarin tsare-tsaren kasafin kudin kasar nan na shekarar 2023 zuwa 2025.

A yayin zaman da kwamitin ya shirya a ranar Talata, Ministar ta baiyana cewa kasafin kudin shekara mai zuwa zai kai naira tiriliyan 19 da bilyan 76, amma kuma za’a samu gibin naira tiriliyan 12 da bilyan  43 a sakamakon harajin shigo da kayayyaki wanda zai lakume naira tiriliyan shida da kuma biyan kudin tallafin mai wanda zai lashe naira 6 .

Ministar Kudi Zainab Ahmed

A sakamakon nuna bacin ran da shugaban kwamitin sanata Olamilekan Adeola yayi, a bisa haka ne ya fadawa ministar cewa  ya zama wajibi a sake  yin nazari kan gibin kudin da ministar  ta baiyana  wanda  tace  dole sai an ranto naira tiriliyan 12 a badi domin cikin kasafin kudin.