On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Najeriya Zata Yi Asarar Dala Milyan 700 A Bana.

IATA LOGO

Kungiyar Masu harkokin Sufurin Jiragen Sama ta Duniya ta ce kamfanonin jiragen sama na Najeriya da sauran wadanda suke a nahiyar Afirka za su yi asarar dala miliyan 700 a shekarar bana, sakamakon yakin da ake kan yi tskaanin kasar Rasha da Ukrain da kuma annobar COVID-19.

Kungiyar ta baiyana haka ne yayin  taronta  shekara-shekara karo na 78 da ake yi a birnin Doha na kasar Qatar.

Kungiyar  ta IATA ta ce hauhawar farashin kayayyaki,da karin kudin  ruwa zai cigaba da shafar harkokin  sufurin jiragen sama a duniya, tana mai jaddada cewa ya kamata kasashe su yi koyi da irin matakan da aka dauka a lokacin da ak samu barkewear  annobar  COVID-19.

Kazalika kungiyar tace  ya zama  wajibi masu ruwa da tsaki su dauki matakan da suka dace domin  magance  matsalolin da suke  kawo katsalandan ga bangaren sufurin jiragen sama a Duniya.