On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Nan Da Shekarar 2030 Najeriya Zata Dena Amfani Da Kananzir

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana sabbin tsare-tsare da gwamnatinsa ta bijiro dasu domin dena yin amfani da kananzir a kasar nan nan da shekara ta 2030, a wani bangare na kudurin da Najeriya ta dauka na samar da yanayi mai inganci da kuma magance dumamar yanayi.

Shugaban ya bayyana hakan ne jiya a yayin wata  tattaunawa da shugaban kasa Amurka Joe Biden ya jagoranta kan babban taron bunkasa tattalin arziki kan samar da  makamashi da sauyin yanayi, wanda aka  gabatar kai tsaye ta hanyar allon gani gaka.

Shugaba Buhari ya zaiyana irin kudaden da kasar nan ke kashewa  wajen tabbatar da kudurorin, cikinsu hadda kara  yawan Motocin Bas da jama’a zasu rika amfani dasu a bangaren sufuri, da bijiro da tsare-tsaren  magance  saran daji da kuma kona shi.

 

 

 

More from Labarai