On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Nasarar Oyebanji Zabin Allah Ce -Dan Takarar PDP A Zaben Ekiti Olabisi Kolawole

‘Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Ekiti, Olabisi Kolawole, ya taya dan takarar jam’iyyar APC Biodun Oyebanji murnar nasarar da ya samu a zaben.

Baturen zaben Kayode Oyebode, shine ya ayyana Oyebanji a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna na jihar ta  Ekiti da  safiyar ranar Lahadi.

A cikin wasikar taya murna, Kolawole ya yi fatan Allah ya ba Oyebanji nasara wajen tafiyar da mulkinsa, inda ya ce nasararsa zabin Allah ce, domin mulki nasa ne.

More from Labarai