Tsawon shekaru, itacen girki, kara da gawayi sun kasance manyan hanyoyin da iyalai da dama ke amfani da su wajen dafa abinci a yankunan karkarar arewacin Najeriya, amma yanzu mazauna Karamar Hukumar Kabo ta Jihar Kano sun fara samun damar yin amfani da wata sabuwar hanyar girki.
Wannan sauyi ya biyo bayan wani shiri na Hukumar Samar da Kayayyakin More Rayuwa ta Hanyar Kimiyya da Kere-Kere (NASENI), wadda ta rabawa mazauna yankin murhun girki mai amfani da makamashi mai tsafta da kuma na'urorin samar da makamashi ta hasken rana.
Shirin na daga cikin kokarin NASENI na inganta fasahohin da aka kirkira a cikin gida domin magance matsalolin yau da kullum, kare muhalli da inganta rayuwar 'yan Najeriya, musamman wadanda ke zaune a yankunan karkara.
Da yake magana a wajen shirin bada tallafi ga mazauna Kabo, Babban Darakta kuma Shugaban Hukumar NASENI, Khalil Sulaiman Halilu, ya ce an samar da murhun girkin ne a cikin gida domin rage sare bishiyoyi, kare muhalli da kuma inganta tsafta da lafiya wajen girki.
Halilu ya ce hukumar ta mayar da hankali wajen fitar da fasahohin da aka kirkira a Najeriya daga dakunan bincike da wuraren samar da kayayyaki, zuwa hannun al'ummomin da za su amfana da su.
Ga mazauna Kabo, wannan tallafi ya samar musu da wata hanyar daban daga hanyoyin girkin da suka dade suna dogaro da itacen girki, kara da gawayi.

Zainab Ahmad, daya daga cikin wadanda suka amfana da tallafin, ta ce a baya yawancin mazauna yankin sun dogara da kara da itacen girki wajen dafa abinci, inda hayaki ke cutar da lafiyar su a mafi yawan lokuta.
Ta ce sabuwar hanyar girkin ta samar musu da madadin da ya fi tsafta, inda ta kara da cewa gawayi na musamman da NASENI ta kirkira tare da murhun sai inganta yadda suke girki.
A cewarta, ana iya amfani da sabon murhun a cikin gida a lokacin damina, yayin da karancin baki da ke taruwa a lokacin girki zai saukaka tsaftace tukwane da sauran kayan girki.
Zainab ta ce, “Yanzu Allah Ya kawo mana mafita ta hannun NASENI,” tana mai bayyana tallafin a matsayin wani sauyi mai kyau ga iyalan yankin.
Wata daga cikin wadanda suka amfana, Fatima Usman Kabo, ta ce sabon murhun zai ba mazauna yankin damar yin girki cikin kwanciyar hankali, tana mai bayyana shi a matsayin babban cigaba idan aka kwatanta da kayan girkin da suke amfani da su a baya.
Baya ga inganta girki a gidaje, ana sa ran shirin zai taimaka wajen kare muhalli ta hanyar rage dogaro da itacen girki.
Wani mazaunin yankin, Sabiu Danlami Kabo, ya ce shirin zai inganta yadda mata ke gudanar da girki tare da taimakawa wajen rage sare bishiyoyi a kauyukan.
Shirin na Kabo ya kuma hada da na'urorin samar da makamashi ta hasken rana, wadanda za su bai wa wadanda suka amfana wata hanyar samun makamashi mai tsafta domin bukatun gidajensu.
A cewar NASENI, hada fasahar girki mai tsafta da makamashin hasken rana na daga cikin kokarin hukumar na samar da fasahohin cikin gida domin magance matsalolin da al'ummomi ke fuskanta a aikace.
Shirin ya samu goyon bayan shugabannin al'umma da na siyasa, inda Dagacin Kabo, Alhaji Bashir Ado Bayero, ya gode wa shugabancin NASENI da Gwamnatin Tarayya bisa abin da ya bayyana a matsayin tallafi mai cike da kyakkyawar manufa.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibril, wanda Shugaban Ma'aikatansa, Farfesa Mohammad Ibn Abdallah, ya wakilta, shi ma ya yaba da shirin, yana mai cewa zai saukaka rayuwa ga iyalai, musamman wadanda ke zaune a yankunan karkara.
Shi ma Daraktan Janar na Kungiyoyin Tallafawa Shugaba Tinubu, Umar Tanko Yakasai, ya yaba da shugabancin Halilu a NASENI, yana mai cewa nasarorin da hukumar ta samu karkashin jagorancinsa sun sanya shi cikin matasan Najeriya masu tasiri tare da kara masa matsayi tare da sanya shi cikin cikin amintattun Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Comments
Add a comment