On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Na'urar Bibas Ce Kadai Aka Wajabta Ma Hukumar Zabe Yin Aiki Da Ita - Kotu

BIBAS

Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa, Ta ce ba dole ba ne Hukumar zabe ta kasa ta rika tura sakamakon zabe kai tsaye ta hanyar amfani da na’ura, Inda ta baiyana cewar Hukumar tana da ‘yancin yin amfani da hanyar da ta yi niyyar yin amfani da ita wajen tura sakamakon zabe.

Kotun ta baiyana cewar, Na’urar tantance masu zabe ta BIBAS ita ce  aka wajabtawa  hukumar zaben ta kasa  yin amfani da ita.

Kazalika kotun ta yi watsi da  zargin da Atiku Abubakar  da jam’iyyar sa  ta PDP  suka yi na cewar,  Tinubu   ba cikakken dan Najeriya ba ne,  kuma  yana da shaidar zama  ta ‘yan kasashe  guda biyu.

Haka zalika kotun ta yi  fatali da zargin da masu kara  suka yin a cewar  Tinubu bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa ba, saboda zarginsa da aikata lefuka a kasar Amurika.