On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

NDLEA Ta Kama Kilo Dubu 155 Na Miyagun kwayoyi

NDLEA

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kwace kilogram Dubu 155 na miyagun kwayoyi Daban-Daban tare kuma da Cafke masu tu’ammali da kwayoyi Dubu 5,341 cikin wata Biyar a fadin kasa

  Shugaban  Hukumar ,  Birgediya  janar  Buba  marwa  mai  Ritaya  shine  ya  shaida  haka  yayin  Taron karawa  juna  sani  na  Dakilewa tare da  bayar  da  Horo  da  kula da  Lafiya   kan  harkokin  da  suka  shafi  tu’amali  da  miyagun  kwayoyi  wanda  aka  shiryawa  matan  Gwamnoni  awani  bangare  na  Bikin Ranar  yaki  da  miyagun  kwayoyi  ta  Duniya  da  ake  Gudanarwa  a  kowacce  Ranar 26  ga  watan  da  muke  ciki  ta  kowacce  shekara ,wanda daya  Gudana  a  Abuja

Kazalika Marwa ya ce taron bitar na da matukar muhimmanci  ga dabarun da ake bi na dakile cin zarafi da fataucin miyagun kwayoyi da kuma illar   dake  tattare  da   shan miyagun kwayoyi a kasar nan, kasancewar an bayyana Nijeriya a matsayin babbar kasa mai nomawa tare da zukar  tabar wiwi.