On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Ni Ba Shugaban Kasa Ne Mai Neman Uziri Ba - Tinubu Ya Fadawa 'Yan Najeriya

Shugaba Bola Tinubu ya fadawa’yan Najeriya cewa shi ba Shugaban kasa ne dake ba da uzuri ba.

Ya ce zai yi aiki tukuru da manufa da jajircewa wajen samar da arziki ga daukacin ‘yan Najeriya.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar masu ruwa da tsaki na jihar Rivers a fadar gwamnati dake Abuja.

Ya ce wani bangare na tsarin tattalin arziki na gwamnatinsa shi ne gyara matatar mai ta Fatakwal da dai sauransu.

Shugaba Tinubu, wanda ya bayyana jihar Rivers amatsayin cibiya ga harkokin tattalin arziki a Najeriya, yace akwai bukatar a cigaba da kyautata tsare-tsare yadda za’a yi daidai da kokarin da gwamnatin tsakiya ke yi wajen  bunkasa Najeriya.

Tsohon shugaban kungiyar lauyoyi a Najeriya, Chukwujinka Okocha, wanda ya zanta da manema labarai bayan kammala taron, ya ce tawagar ta bukaci a gyara hanyar gabashi zuwa yamma, wadda ta kai har matatar Fatakwal domin saukaka jigilar kayayyakin man fetur.