On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Ni Na Ajiye Aiki Da Kaina, Ba Ganduje Ne Ya Kore Ni Ba- Baba Impossible

Tsohon kwamishinan harkokin addinai a jihar Kano, Dr Muhammad Tahar Adam da akafi sani da Baba Impossible yace ya yi murabus ne bisa radin kansa, inda ya musanta rahoton cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ya sauke shi daga kan mukaminsa.

Idan dai za a iya tunawa, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba ya fitar da wata sanarwa a ranar Asabar inda ya sanar da korar Dr Muhammad Tahar Adam a matsayin kwamishinan harkokin addinai. 

Sai dai  wata tattaunawa da wata kafar yada Labarai  a Kano, Baba Impossible ya bayyana mamakinsa kan labarin korarsa inda ya bayyana cewa ya mika takardar murabus dinsa a ranar Juma’a, 30 ga watan Disamba na shekarar 2022 ga sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji. 

Ya kara da cewa yaje ofishin shugaban ma’aikata, kuna shima ya karba ya  sanya hannu.

More from Labarai