On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

NIHSA Ta Gargaɗi Jihohi 17 Kan Ambaliya

Hukumar kimiyyar ruwa ta ‘Kasa ta fitar da gargaɗin yiwuwar ambaliya na kwanaki bakwai, tana mai cewa akwai matsakaicin haɗarin ambaliya a jihohi 17 tsakanin 21 zuwa 27 ga watan Yuli.

Hukumar ta ce gargaɗin ya biyo bayan tumbatsarruwa a manyan wuraren da ake sa ido da koguna, al-amarin da ke ƙara yiwuwar ambaliyar.

Darakta Janar na hukumar kimiyyar ruwa, Umar Mohammed, ne ya bayyana hakan a cikin Takardar Shawarar Ambaliya ta Ƙasa da aka fitar a jiya.

Ya lissafo jihohin da abin ya shafa da suka haɗa da Adamawa, Bauchi, Benue, Borno, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi, Nasarawa, Neja, Filato, Taraba, Yobe da Zamfara.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 35°C | Low: 23°C