On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Nijeriya Ta Siyarwa Portugal Man Gas Na Dala Bilyan Daya A Bana

KANFANIN MAI

Kanfanin sarrafa Albarkatun mai na kasa , yace , Ya siyarwa Kasar Portugal Gas na kimanin Dala Bilyan 1 a bana.

An baiyana haka ne yayin wani taron tatttaunawa kan harkokin  kasuwanci tsakanin Najeriya da Portugal, wanda aka gudanar a wani bangare na ziyarar da shugaban Kasa Muhammadu Buhari keyi a kasar.

Shugaban kanfanin  mai na kasa Mele Kyari Yace Najeriya Ta dauki tsawon lokaci tana siyarwa kasar Man Gas, kamar yadda ya baiyaan haka a shafinsa na twitter.

Kazalika Taron ya  kuma tattauna kan harkokin da suka shafi Diplomasiyya da kuma harkokin ilimi tare da inganta alakar kasashen biyu.