On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

NLC Ta Musanta Cewar Za Ta Fara Yajin Aiki

Kugiyar Kwadago ta NLC ta musanta wasu rahotanni dake baiyana cewar, tana shirin fara yajin aiki daga yau, saboda janye tallafin mai da gwamnatin taraiyya ta yi.

A  ranar larabar  data  gabata  ce, aka  tashi  batare da cimma wata  matsaya  ba  tsakanin wakilan gwamnatin taraiyya  da kuma  shugabannin kungiyoyin kwadago, a  yayin  ganawar  da suka  yi  kan    batun cire  tallafin mai.

Biyo  bayan wannan  labari  ne, wasu rahotanni  suka  fara  yawo  na  cewar  kungiyar  ta NLC  ta saka  yau juma’a  a matsayin ranar  da zata  soma yajin aiki, domin nuna  bacin ranta  kan janye  tallafin man.

Sai dai  a raddin da  kungiyar  ta NLC  ta  yi,  ta hannun kakakinta  Benson Upah,  Ya  yi kira  ga  ‘yan Najeriya  da suyi  watsi da rahotannin,  inda  ya  ce kungiyar  tasu  zata  cigaba da  sanar da al’umma  halin da ake  ciki, da kuma irin matakin da zata dauka,  bayan  kammala  ganawarta  da wakilan gwamnatin taraiyya a  yau.