On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

NLC Ta Umarci 'Ya'yanta Su Koma Bakin Aiki

NLC

Kungiyar kwadago ta NLC ta sanar da kawo karshen yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyu data gudanar, inda ta bukaci ‘ya’yan kungiyar dasu koma bakin aiki daga yau Alhamis.

Shugaban kungiyar na kasa, Joe Ajaero  ya yabawa ma’aikatan kasar  saboda  shiga yajin aikin da suka yi, inda y ace  an cimma babbar  nasara.

Yan kwadagon sun tafi  yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyu a ranar Talatar data  gabata, saboda rashin cika masu alkawarun da gwamnati  ta dauka kan batun janye  tallafin mai  da aka yi.