Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) reshen Jihar Kano ta buƙaci ma’aikatan gwamnati da jinkirin albashi ya shafa da su kwantar da hankalinsu, tana mai cewa matsalar ta samo asali ne daga tangarɗar fasaha da bankin da ke kula da biyan albashin ya fuskanta.
Shugaban NLC na jihar, Kabiru Inuwa, ya ce matsalar ta sa wasu ma’aikata suka karɓi albashinsu sau biyu, yayin da bankin ya cire ƙarin kuɗin daga asusun wasu.
Ya ce Ofishin Shugaban Ma’aikata, Akanta Janar na jihar da kuma Sakataren Gwamnatin Jihar na ci gaba da aiki domin magance matsalar.
NLC ta kuma yaba wa ma’aikatan da suka mayar da albashin da aka biya musu sau biyu bisa kuskure, tare da jinjinawa Gwamnatin Jihar Kano kan ci gaba da biyan albashin ma’aikata a kan lokaci.
Comments
Add a comment