On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

NLC Ta Zargi 'Yansanda Da Lakadawa Shugabanta Duka.

JOE AJAERO

Kungiyar kwadago ta kasa ta zargi rundunar ‘yansanda ta kasa da lakadawa shugabanta na kasa Joe Ajaero duka, bayan sun yi awon gaba dashi a tsakar ranar jiya a jihar Imo.

Shugaban yada  labarai da hulda da jama’a na kungiyar, Benson Upah  shine ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa  da  ya fitar a daren jiya, lokacin da yake tabbatar das akin shugaban nasu, bayan ya wuni a hannun jami’an yansanda.

Jami’an yansanda  sunce  sun tsare  shugaban kungiyar  kwadagon ta  kasa ne domin bashi kariya  bayan ya fuskanci  cin zarafi.

Sai dai jim kadan da sakin shugaban kungiyar  kwadagon ta kasa  kwamared  Joe  Ajaero  ya tabbatar da cewar  an lakada masa  duka sannan aka yi awon gaba dashi zuwa  wani  wuri da bai sani, wanda a nan ne aka gallaza  masa.