On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Obasanjo Ya Koka Da Tsadar Man Dizal A Najeriya

Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Ya koka game da tsadar Man Dizal, inda yace al’amarin na shafar kasuwancinsa.

Obasanjo wanda ya baiyana haka a ranar Talata, Yayin wani taron masu sana’ar kiwon Kifi na yankin Kudu maso yammacin kasar nan, Yace  tsadar da man dizal da kuma kayan abincin  kiwon kifi  suka yi a kasar nan, zai sa masu sana’ar kiwon kifi da dama barin sana’ar, har sai dai idan sun yadda da yadda farashin abubuwan yake kasancewa.

Ya kara da cewa a yadda ake siyar da  litar man dizal kan naira 800 a halin yanzu, sannan kuma Kilo 1 na kifi yana kaiwa 1400  babu wata  riba  da mai sana’ar kiwon kifi zai samu, har sai idan ya sayar dashi kan naira  1500 ko kuma sama da haka.