Farfesa Is-haq Oloyede ya miƙa ragamar shugabancin Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ga Farfesa Segun Aina, wanda ya zama sabon magatakardar hukumar.A wajen bikin miƙa mulki, Oloyede ya gode wa ma’aikata da masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suka ba shi, yana mai bayyana wa’adinsa na shekaru goma a matsayin lokaci na sauye-sauye, gaskiya da bunƙasa hukumar. Sabon magatakardar, Farfesa Segun Aina, ya yi alƙawarin kare martabar JAMB, inganta ayyukanta da kuma amfani da fasaha domin ƙara inganci da gaskiya wajen gudanar da ayyukan hukumar. Aina ya karɓi ragamar shug
A wajen taron, Oloyede ya gode wa ma’aikata da masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suka ba shi, yana mai bayyana wa’adinsa na shekaru goma a matsayin lokaci na sauye-sauye, gaskiya da bunƙasa hukumar.
Sabon magatakardar, Farfesa Segun Aina, ya yi alƙawarin kare martabar JAMB, inganta ayyukanta da kuma amfani da fasaha domin ƙara inganci da gaskiya wajen gudanar da ayyukan hukumar.
Aina ya karɓi ragamar shugabancin hukumar ne bayan Oloyede ya kammala wa’adinsa na zangon mulki biyu, kuma yanzu shi ne zai jagoranci tsarin shigar ɗalibai manyan makarantu a Najeriya.
Comments
Add a comment