On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

PDP ta lashe zaben kananan hukumomi a Adamawa

Shattima ya yabawa al’ummar jihar da jami’an tsaro da...

Article body: Jam’iyyar PDP tayi nasarar lashe baki daya kujerun kananan hukumomi 21 a zaben shugabannin kananan hukumomi da aka gudanar na jihar Adamawa a karshen mako.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Adamawa Isah Shattima shine ya sanar da sakamakon zaben a shalkwatar hukumar dake birnin Yola.

Shattima ya yabawa al’ummar jihar da jami’an tsaro da suaran masu ruwa da tsaki bisa hadin kai da suka bayar wajen kammala zaben cikin nasara.

Tuni aka mika shaidar zaben ga wadanda sukayi nasara da maraicen ranar  lahadi.

Sai dai a wani martani na gaggawa game da sakamakon zaben, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yace nasarar jam’iyyar ta nuna cewa PDP ce zabin ‘yan Najeriya.