On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Ranakun Komawa Makaranta Na Nan Daram - Gwamnatin Jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano ta musanta duk wasu rahotanni da ake yadawa cewa an tsawaita lokutan komawa makaranta ga dalibai

Wata sanarwa da daraktan wayar da kan al'umma Aliyu Yusuf ya fitar tace, an jawo hankalin ma’aikatar ilimi ta jihar Kano kan wata sanarwa da aka yada cewa an tsawaita ranakun komawa makarantu daga hutun zango na 3 da mako guda. 

Masu yada  wannan jita-jita waɗanda a koyaushe suke son haifar da ruɗani a cikin zukatan iyaye  duk lokacin da  hutu yazo ƙarewa.

Saboda haka ma'aikatar ilimi ke jan hankalin iyaye da masu kula da yara da daliban makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar Kano  cewa  za a koma makarantun kwana  ranar Lahadi 11 ga watan Satumba yayin da na ranar  12 ga watan na Satumba 2022.

Haka kuma sanarwa da Aliyu Yusuf  ya fitar, ta ce, yayin da take gode wa iyaye da masu kula da yara  bisa goyon baya da hadin kai, ma’aikatar ta bukace su da su tabbatar da yin biyayya ga ranar komawa makarantu saboda akwai hukunci dake jiran wadanda suka gaza bin umarnin komawa.