On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Ranar Lahadi Za’a Fara Jigilar Maniyatan Sokoto Zuwa Kasar Saudiyya

Gwamnatin Jihar Sokoto ta ce za ta fara jigilar maniyata zuwa aikin hajjin bana daga yau Lahadi.

Babban sakataren zartaswa hukumar kula da jin dadin alhazai a jihar, Shehu Muhammad Dange, shi ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai ranar Asabar.

Shehu Muhammad ya ce jihar na da adadin maniyyata 2,404.

Ya ce tuni hukumar ta samar wa maniyata 1,000 biza da kuma kudaden guziri.

 Ya kara da cewa an yi wa dukkan maniyatan jihar allurar rigakafin Covid-19.

Gwamnan jihar ta Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya nada kakakin majalisar dokokin jihar a matsayin shugaban tawagar alhazan a aikin hajjin na bana.