On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Rikicin Makiyaya Da Manoma A Jihar Kano [JIGON RAHOTON MU NA MAKO]

Rikicin Manoma da Makiyaya a Arewacin kasar nan ba bakon al’amari ba ne, Sai dai Jihar Kano ba ta fuskanci irin wannan matsala ba, in banda ‘yan kwanakin nan da matsalar ta kunno kai har ta kaiga asarar rayuka.

Kamar yadda aka saba, Ana cigaba da nuna ‘dan yatsa kan kutse da ake yiwa gonakin da kuma Lalata Amfanin da aka noma, A yayin da wadanda abun ya shafa  ke cigaba da kididdige  irin asarar da suka yi.

Wannan matsala ita ce abunda jigon rahotonmu na wannan makon da wakilinmu Kamaluddden Muhammad yayi duba a kanta, inda ya gana da wasu daga cikin wadanda abun ya shafa dama su kansu makiyayan da sauran masu ruwa da tsaki.

Ga cigaban rahoton daga  bakinsa

More from Labarai