On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Rikicin Siyasar Jihar Ondo A Najeriya Na Kara Daukar Sabon Salo

Magoya bayan mataimakin gwamnan jihar Ondo, Hon Lucky Aiyedatiwa da na gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, na shirin gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a Akure, babban birnin jihar Ondo, a cikin makon nan.

Magoya bayan mataimakin gwamnan sun sanar da shirye-shiryen zanga-zangar a shafukan sada zumunta daban-daban a karshen mako, kamar yadda magoya bayan Akeredolu suma suka sha alwashin gudanar da zanga-zangar adawa.

Dan majalisar wakilai Kokade Akinjo ne ke jagorantar zanga-zangar adawa da Akeredolu.

Sai dai , wata kungiya a jihar am ta yi kira ga magoya bayan gwamnan da mataimakinsa da su maida takubansu cikin kube  domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.