On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Rukunin Farko Na Maniyyatan Najeriya Sun Sauka A Birnin Madina

Jirgin dauke da maniyata 472 daga jihar Nassarawa da jami'ai 27 ya sauka a filin jirgin saman  Muhammad Ibn Abdu-Azeez dake Madina da  karfe 3:20 na dare.

Jakadan Najeriya a kasar Saudiyya,  Ambasada Yahaya Lawal tare da karamin jakadan Madina, da tawagarsa sun kasance a filin jirgin saman domin tarbarsu. 

A bisa al'ada ma'aikatar aikin hajji da umrah ta kasar Saudiyya da jami'an ofishin jakadancin Najeriya a kasar sun yi shiryawa maniyyatan liyafar tarba a filin jirgin saman.

Suwaiba Ahmed dake sashen yada Labarai da wallafa bayanai a hukumar NAHCON ta rawaito a jawabinsa na  maraba, Ambasada Yahya Lawal ya godewa Allah da ya sauki matafiyan  lafiya, ya kuma bukace su da su kasance jakadu nagari ga Nijeriya a kowane lokaci. 

Ya kuma yi kira gare su da su yi addu’a don cigaba da hadin kan Nijeriya. 

Daga karshe kuma a yi musu addu'ar yin ibadar Hajji karbabbiya.

Daga nan aka kai maniyyatan masaukinsu.