On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Rundunar Soji ta Kasa Ta Musanta Cewar Dakarunta Zasu Yi Zanga-zanga

Rundunar soji na kasa ta sake musanta zargin cewar jami’anta na shirin Gudanar da zanga-zanga asakamakon tabarbarewar yanayin aiki da kuma Rashin biyansu hakkokinsu .

Koda a  Ranar 18  ga  watan Mayun Bana, Rundunar  ta  sake  karyata irin  wannan  ikirari.

 Kazalika  cikin  wata  sanarwa  da  Daraktan  yada  labaran  Rundunar,  Birgediya  janar  Onyema  Nwanchukwu  ya  fitar  ya    baiyana  ikirarin  amatsayin  wanda  babu  kanshin  Gaskiya  acikinsa wanda kawai aka  kirkira domin batawa rundunar suna

  Ya  kuma  zargi  duk  wadanda  suke  ikirarin  da  kokarin  haifar  da  Rudani  atsakanin  jami’anta

  Bugu  da  kari,  Onyema  ya  kara  da  cewa    awani  banagare  na  inganta  ayyukan  jami’an,  Rundunar  ta  samar  da  wani  tallafi  karkashin  shugabancin  RUNDUNAR  SOJI  TA  KASA  domin inganta walwalar dakarun