On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

Rundunar Sojin Najeriya Ta Gargadi Masu Shirin Kawo Tarnaki Wajen Mika Mulki Ga Sabuwar Gwamnati

A karo na biyu, Rundunar sojin kasar nan ta yi gargadin shirya kowace irin makarkashiya domin kawo tazgaro wajen mika mulki ga zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, a ranar 29 ga watan da muke ciki.

Daraktan yada labarai na  shalkwatar  tsaro  ta kasa, Manjo Janar Musa  Danmadami,shi  ne  ya yi gargadin, Wata  daya ke nan bayan da daraktan yada labarai na rundunar soji ta kasa, Birgediya  janar  Tukur  Gusau  ya ci alwashin cewar  rundunar  zata  dakile duk wani yunkuri  na kawo  tazgaro ga tsarin dimukuradiyyar  kasa.

Wasu daga cikin ‘Yan takara  da suka harzuka  sun kalubalanci  rantsar  da zababben shugaban kasar  tare  da  yin kira  da a kafa gwamnatin rikon kwarya a  Najeriya.

Sai dai da yake yiwa manema Labarai jawabi a shalkwatar  tsaro ta kasa  dake  Abuja,  Janar  Danmadami, ya  ce sojoji sun shirya  tsaf  domin  tabbatar da cewar  babu wata kitimurmura da aka kulla  domin kawo  nakasu  ga mika  mulkin.