On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Rundunar Sojojin Ruwa Ta Najeriya Ta Nesanta Kanta Daga Shirin Daukar Aiki Na Bogi

Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta bukaci jama'a da su yi watsi da sakon daukar ma'aikata da ke yawo a shafukan sada zumunta. 

Daraktan Yada Labarai na Rundunar Sojin Ruwa, Commodore Adedotun Ayo-Vughan a wata sanarwa da ya fitar ya bayyana batun daukar aikin amatsayin na karya da yaudara. 
Ayo-Vughan ya nunar da  cewa an shawarci jama'a da su yi taka tsantsan don kaucewa fadawa hannun  masu laifi da 'yan damfara da ke da hannu wajen kitsa daukar ma'aikata na karya. 
Kakakin rundunar sojin ruwa ya kara da cewa shirin daukar ma'aikata da sojojin ruwan Najeriya ke gudanarwa ana yada shi yadda ya kamata kuma ana sanarwa  a shafukan na Ainihi na rundunar da kafofinta na  sada zumunta.