On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Rundunar Sojojin Saman Najeriya Ta Nesanta Kanta Daga Harin Bama-Bamai A Jihar Kaduna

Rundunar sojin saman Najeriya ta yi watsi da rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani na cewa jiragenta sun  kai wani hari ta sama wanda ya kai ga kashe fararen hula bisa kuskure a jihar Kaduna.

Kakakin Rundunar Sojojin Sama, Air Commodore Edward Gabkwet a wata sanarwa  ranar Litinin, ya ce rundunar ba ta gudanar da wani aiki a Kaduna ko kewaye cikin sa’o’i 24 da suka gabata ba.

A cewarsa, ba rundunar  ce kadai ke gudanar da jiragen yaki marasa matuka ba a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

Ya kuma yi kira da a yi taka-tsan-tsan kafin a wallafa rahotannin da ba a tabbatar da su ba a kafafen yada labarai.