On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Rundunar 'Yan Sanda A Jihar Zamfara Ta Kama Masu Buga Jabun Kudi Na Takardun Naira Da Dala

An kama wasu mutane 3 da ake zargi da buga kudin dala a jihar Zamfara inda suka kware wajen  buga takardun kudi na bogi a jihar.

Rahotanni sunce jami’an hukumar tsaro mai bada kariya ga fararen hula ne suka kama wadanda suka aikata laifin.

Da yake holen wadanda ake zargin a ranar Laraba a Gusau, Kwamanda hukumar Muhammad Bello Muazu ya ce an kama wadanda ake zargin ne da laifin bugawa da kuma kashe takardun kudin bogi   na Naira da Dalar Amurka a jihar ta Zamfara.

Kwamandan ya shawarci jama’a da su yi hattara da miyagun mutane domin idan aka kama su za’a gurfanar da su a gaban kotu.