On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Rundunar Yan Sandan Kano ta Maida Martani Kan Zargin Muzgunawa Masu Adawa da Tinubu

Kungiyar ‘Tinubu Must Go’ (TMG) ta zargi rundunar ’yan sandan jihar Kano da take hakkin kundin tsarin mulkin kasa, bayan tura jami’an ’yan sanda dauke da makamai domin hana mambobinta shiga wurin taron da suka shirya gudanarwa jiya.

Wani lauya masanin kundin tsarin mulki da ke Kano, Abba Hikima, wanda yana daga cikin manyan masu shirya taron, ne ya yi zargin a wani bidiyo  da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.

A cikin bidiyon, Hikima ya ce an tura motoci sama da goma na rundunar ’yan sandan, inda aka toshe hanyar da za ta kai ga cibiyar taron mai zaman kanta.

Ya ce gwamnatin Tinubu na tsoron barin taron ya gudana, domin hakan zai nuna irin yadda jama’a ke son ganin karshen gwamnatin da ya ce ta jefa su cikin matsin rayuwa.

Da yake mayar da martani, kwamishinan ’yan sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce matakin ya samo asali ne daga damuwa kan tsaron mambobin kungiyar TMG da sauran mazauna jihar.

A wata hira da aka yi da shi jiya, CP Bakori ya amince cewa ya kamata kungiyar TMG ta sanar da ’yan sanda tun da wuri, domin su samar da tsaro da kuma kauce wa duk wani abu da zai iya kawo barazana ga zaman lafiyar jihar.

Ya ce rundunar ta damu da taron ne saboda yawan mutanen da ake sa ran za su halarta.

Da aka tambaye shi ko rundunar na da bayanan da ke nuna cewa mutane 700 da ake sa ran za su halarci taron suna da tarihin aikata laifuka, Bakori ya ce rundunar na daukar matakan kandagarki domin kauce wa duk wata barazana ga zaman lafiya.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 38°C | Low: 21°C