On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Zamfara Ta Ce Har Yanzu Bata Karbi Umarnin Bada Lasisin Rike Bindiga Ga Al’umma Ba.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Ayuba Elkana ya ce har yanzu dokar hana mallakar bindiga tana nan daram a jihar.

Elkana ya bayyana hakan ne amatsayin martani ga umarnin da gwamnatin jihar ta bayar na cewa rundunar ‘yan sanda zata bada lasisin mallakar bindiga ga wadanda suka cancanci rike makamai.

Ya ce har yanzu bai samu wani umarni na bada  lasisin bindiga ga jama’a ba.

Idan dai za a iya tunawa, a wata sanarwa da gwamnatin jihar Zamfara ta fitar a ranar Lahadi, ta umurci mazauna jihar da su mallaki bindiga domin kare kansu daga ‘yan ta’adda da ke addabar jihar.