On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Sha Alwashin Daukar Mataki Kan Magoya Bayan ‘Yan Siyasa Dake Kalaman Barazana Ga Abokan Adawa

Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta ja hankalin daukacin ‘yan siyasa akan su gargadi magoya bayansu game da yiwa bangaren adawa barazana da furta kalamai masu zafi yayinda ake tunkarar manyan zabukan 2023.

Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi shine ya yi wannan gargadin  a ranar Lahadi biyo bayan cin zarafi da ake fuskanta ta kafafen sadarwar zamani da kuma musayar kalamai tsakanin  magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu da kuma na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi.

Adejobi ya ce duk wata barazana ga rayuwa laifi ne, inda ya kara da cewa dokar zabe ta fito karara tayi bayani akan hukuncin da ya dace da aka tanada kan laifukan da suka shafi zabe.

Ya ce ‘yan sanda ba za su zuba idanu ana karya dokar zabe ba, saboda haka ya shawarci duk wanda ya ji an yi masa barazana ya kai rahoto ga ‘yan sanda domin daukar matakin da ya dace.