On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Rundunar Yansanda Ta Bukaci 'Yan Najeriya Su Dena Nuna Shakkunsu Kan Zabe Mai Zuwa

YAN SANDA

Sufeton ‘yan sanda na kasa, Usman Alkali-Baba ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su nuna shakkunsu kan yuyuwar gudanar da babban zaben kasar nan dake tafe.

Babban sufeton ‘yansandan  ya baiyana haka ne a  ranar Litinin a birnin Badunin a  wajen bikin bude taron kwanaki hudu da aka shirya wa jami’an hulda da jama’a na ‘yan sanda a  fadin kasar nan.

Alkali-Baba ya ce rundunar ‘yan sanda tare da hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro za su tabbatar da gudanar da sahihin zabe a shekarar  2023 cikin adalci da batare da wata katsalandan ba.

Daga nan sai ya bukaci daukacin jami’an hulda da jama’a na rundunonin yansanda dasu  kasance masu kyakykyawar alaka bawai ga iya magana kadai ba, harma da iya hulda da halaiyar mutane daban- daban.