On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Rundunar 'Yansanda Ta Kama Jami'anta Dake Gadin Mawaki Rarara

Rarara

Shalkwatar rundunar ‘yansanda ta kasa ta tabbatar da kama wasu jami’an yansanda guda ukku da aka gani cikin wani faifan bidiyo suna yin harbi cikin iska a lokacin da suke tare da fitaccen mawakin siyasar nan,Dauda Adamu Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara.

Jami’an yansandan  sun hada da Sergent Abdullahi Badamasi  da Segernt Isah Danladi da  kuma  Insifekta Dahiru  Shu’aibu, wadanda sune ke tsaron lafiyar  fitaccen mawakin.

An samu jami’an ‘yansandan suna harbi da  bindiga  kirar  Pistol da kuma  kirar  Ak 47 a  lokacin da suke  raka  mawaki Rarara  domin ya  shiga  cikin motarsa  a wajen wani rabon kayan  abinci  da  ya yi a mahaifarsa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar  yansanda  ta kasa, CSP Olumiyiwa Adejobi shine ya tabbatar da kama jami’an yansandan  a shafinsa na twitter, Ya  ce  a yanzu haka suna  hannunsu, kuma yayi alkawarin yin cikakken jawabi  da zarar  an  kammala gudanar da binciken da za’a yi masu.