On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Rundunar Yansanda Ta Kori Dogarawan Rarara Daga Bakin Aiki

Rarara

A ranar Laraba ne rundunar Yansanda Ta fitar da sanarwar kama jami'an yansanda domin yin bincike a kansu.

Rundunar ‘yansanda  ta kasa  ta  kori jami’an ‘yansandan  nan dake tsaron  lafiyar  fitaccen mawakin siyasar nan, Dauda Adamu Kahutu Rarara saboda samunsu da lefin  barnatar da harsashin bindiga  a  wofi.
Kakakin  rundunar  yansanda  ta kasa,Olumiyiwa  Adejobi ne  ya  baiyana  matakin da rundunar  ta dauka a shalkwatarta dake  Abuja  ranar Alhamis,  biyo bayan kammala  binciken da aka yi kan jami’an yansandan da abun  ya  shafa.
Dogarawan  Mawakin da abun ya shafa  sun hada da Sergent Abdullahi Badamasi  sai  Sergernt Isah Danladi  , wanda  aka gansu a cikin wani faifan bidiyo da aka dauka a ranar  7 ga watan da muke ciki, Suna yin harbi cikin iska  a lokacin da suke tare da mawakin siyasar.
Adejobi  ya  ce an sallami  jami’an yansandan  ne  saboda  nuna rashin da’a da  kuma  yin amfani da  bindiga a wurin da bai  kamata ba,  da  kuma  bata  harsashin bindiga