Sama da gidaje 200 ne suka fadi bayan ruwan da aka yi kamar da bakin kwarya, hadi da iska mai karfi a Dutse, babban birnin jihar Jigawa ranar Asabar din da ta gabata.
Ruwan saman, wanda ya shafe sama da sa'a guda, bayan da ya fara sauka tun daga karfe 8 na safe, ya haifar da ambaliyar ruwa a sassan birnin da dama da suka hadar da Dan Masara, titin zuwa fadar gwamnatin jihar da kuma Takur.
Da yake zantawa da Arewa Radio, wani mazaunin birnin, Abdullahi Kamilu, yace ambaliyar ruwan ya lalata wuraren zaman jama'a, makarantu, wuraren kasuwanci, masallatai da kuma turakun wutar lantarki da dama.
Wakilin mu Haruna Ahmad Bultuwa, ya rawaito mana cewa gwamnatin jihar ta raba kayan aiki irin su barrow, manjagara da shebur ga mazauna birnin domin rage tasirin ruwan da kuma buda masa hanya.
Birnin Dutsen jihar Jigawa na daga cikin biranen kasar nan da aka yi hasashen samun ambaliyar ruwa a wata kididdiga da hukumomin gwamnati suka fitar a shekarar 2025, inda suka kara da cewa akalla wuraren zaman al'uma 148 barazanar za ta iya shafa a cikin kananan hukumomi guda 17.
Comments
Add a comment