On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Sabanin Lokutan Baya Kasafin Kudin 2024 Zai Fuskanci Taza Da Tsifa - Philip Agbese

Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Philip Agbese, ya ce kasafin kudin 2024 ba zai fuskanci wani nau'i na rubanya ayyuka ba.

Da yake magana a wani gidan talabijin  ranar Alhamis, ya ce za’a tantance kididdigar kasafin kudin shekarar 2024 fiye da yadda aka saba yi a Majalisar Dokokin kasarnan da ta gabata.

Yace ‘yan majalissar na duba yadda za a yi abubuwa daban da yadda aka yi a baya.

Agbese ya ce za’a yi amfani da doka wajen magance dukkanin matsaloli, kuma yayin da suka yi alkawarin yin nazari sosai kan kasafin, za’a tabbatar da ganin ba’a rubanya ayyukan da suka shigar a lokutan baya ba a kasafin kudin 2024.