On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Sabuwar Gwamnatin NNPP A Kano Na Gurgunta Harkokin Kasuwanci - APC

Jam’iyyar  APC  reshen jihar Kano ta yi Allah wadai da aikin rusau da gwamnatin jam’iyyar  NNPP  ke gudanarwa a  jihar Kano, wanda  ta baiyana amatsayin rusa tattalin arziki.

A wani taron manema labarai da jam'iyyar ta gudanar, ta zargi gwamnatin Kano da wuce gona da iri wajen daukar wannan mataki.

Mataimakin shugaban jam'iyyar Alhaji Shehu Maigari ya bukaci wadanda aka rusa wa kadaori su dauki matakan sharia domin kwato hakkokinsu.

Ya ce matakin gwamnatin Kano ya sanya matasa shiga ayyukan bata gari ta hanyar sace-sacen dukiyar Jama'a da lalata kadarori.

Tunda farko sabon gwamnan  Kano Abba Kabir Yusuf da kansa ya jagoranci rushe wasu gine-gine da gwamnatin tace  an yi su ba bisa kaida ba.

To sai dai Alhaji Shehu Maigari ya ce ba gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ce ta fara raba filaye a Kano ba,inda ya bukaci iyayen yara su gargadi yayansu dake dace-sace da sunan dibar ganima.

Ya ce rushe gine-ginen da aka  tanadar  domin amfanin jama’ar jihar Kano abun sosa zuciya ne,  Inda  ya yi kira  ga ‘yan kishin kasa  da  su yi addu’a,  kasancewar  mutane suna tafka gagarumar asara ta bilyoyin naira  a halin yanzu.

Ya kara da cewa, Rusau din ya  gurgunta  harkokin kasuwanci musamman a  kasuwannin Kantin Kwari da Kofar Wambai da sauran wuraren kasuwanci a jihar Kano.

Haka kuma ya yi kira ga hukumomin tsaro a jihar Kano su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.