On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Hukumar Gyaran Hali Ta Bayyana Sharuda Kafin Sakin Tsoffin Gwanonin Da Buhari Ya Yiwa Afuwa

Mai shari’a Adebukola Banjoko na babbar kotun birnin tarayya

Kwanaki biyar bayan majalisar magabatan kasarnan  ta yi wa wasu mutane 159 afuwa, tsohon gwamnan jihar Filato, Sanata Joshua Dariye da Tsohon Gwamna Jolly Nyame na Jihar Taraba da wasu mutane 157 har yanzu ba su shaki iskar ‘yanci ba.
 
Rahotonni sun  nuna cewa ba za a sake su daga cibiyoyin gyaran hali da ake tsare da su ba har sai Ministan Shari’a kuma Atoni-Janar na Tarayya Abubakar Malami ya ba da izini. 

Mai shari’a Adebukola Banjoko na babbar kotun birnin tarayya ya samu Dariye da Nyame da laifin badakalar kudi a  shekarar 2018 da  suka kai Naira billiyan 1.162 da billiyan 1.6.

Sai dai da yake magana kan ci gaba da tsare wadanda aka yankewa hukuncin, kakakin hukumar kula da gidajen gyaran hali ta kasa reshen babban birnin tarayya, Humphrey Chukwuedo, ya ce an jinkirta sakin su ne saboda ba'a samu  amincewar Ministan Shari'a ba.