On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Sama Da Fursunoni Dubu 50 Ke Tsare A Gidajen Gyaran Hali Na Najeriya

A Yanzu haka yawan fursunoni da cibiyoyin gyaran hali a kasar nan suke dauke dasu yakai dubu 58 da 278 a maimakon Dubu 16,000 da ya kamata su dauka.

Da yake jawabi a yayin wani horon kara sanin makamar aiki da aka shirya  a Sokoto birnin shehu, Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali na Kasa, Haliru Nababa ya bayyana cewa an shirya  bitar ne domin kara daidaita yadda ake tafiyar da aiyukan hukumar .

A yanzu haka, gwamnatin tarayya ta umurci hukumar kula da gidajen  gyaran hali na kasar nan dasu tabbatar da an sake kama dukkan fursunonin da suka tsere daga wuraren da aka tsare su cikin gaggawa.