On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Sama Da Tan 400 Na Shara Muka Kwashe A Sassan Jihar Kano - Garo

Kwamitin hadin karta kwana kan aikin kwashe shara a cikin birnin Kano ya yi nasarar kwashe fiye da Tifa dari hudu cikin sa'o'i 72.

Babban sakataren ma’aikatar muhalli ta jihar Kano Alhaji Aliyu Yakubu Garo shine ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin ziyarar dubawa da kuma sa ido kan yadda ake kwashe sharar a cikin kwaryar birni.

Wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar Ismail Garba Gwammaja ya sanyawa hannu, ta ce babban sakataren wanda ya ziyarci wurare kusan 20 a cikin birnin Kano ya bukaci mazauna jihar da su tallafawa kokarin gwamnati na ceto muhalli daga hatsarin sauyin yanayi.

A cewarsa, gwamnati mai ci ta nuna sha’awarta da kuma himma wajen kare rayuka ta hanyar inganta tsaftar muhalli da kuma kudirin wajabta sanya kwando ga direban mota da sauran sabbin tsare-tsare.