On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Sanata Barau Na Yunkurin Dakatar Da Ficewar Kantin Shoprite Daga Jihar Kano

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, na yin wani yunkuri na dakatar da matakin Kantin Shoprite, na rufe reshensa daya tilo a jihar Kano.

Idan za’a iya tunawa Shoprite a makon da ya gabata ya sanar da matakinsa na ficewa daga Kano a watan Janairun 2024 bayan shafe shekaru 9 tun daga 2014, yana mai dora alhakin hakan  a kan kalubalen tattalin arziki.

Wata sanarwa da mai baiwa Sanata Barau shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a Ismail Mudashir ya fitar a yammacin ranar Litinin, ta ce mataimakin shugaban majalisar dattawan zai gana da mahukuntan kamfanin a cikin makon nan a Abuja kan al’amarin.