On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Sanata Dino Melaye Yace Tinubu Bazai Iya Cin Zaben Shugaban Kasa, Saboda Gazawar Shugaban Kasa Buhari

DINO DA TINUBU

Sanata Dino Melaye wanda ya kasance Mai magana da yawun Dan Takarar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, Yace rashin katabus din da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke dashi, Ya cutar da damar da Asiwaju Bola Tinubu keda ita na bashi damar zama shugaban kasa.

Dino wanda ya baiyana haka yayin hirarsa da gidan Talabijin na Channels  ta cikin shirinsu na  Siyasa a yau, Yace  gazawar  jam’iyyar  APC mai mulkin kasa wajen warware  matsalolin tattalin  arzikin kasa dake addabar  Najeriya, Hakan tasa daukacin ‘yan takarar da  jam’iyyar ke dasu ba zasu yi kasuwa a tsakanin ‘yan Najeriya ba.

A wani bangaren kuma, Shugaban Gamaiyyar  kungiyoyin  yada  manufofin Asiwaju da kuma Shettima ta kasa, Adebayo Shittu, Ya baiyana kalaman Sanata Dino Melaye, a matsayin wani abu na nishadi , inda yace  Tinubu ne dan takarar shugaban kasa bawai Shugaban kasa Buhari ba.