On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Sanata Godswill Akpabio Ya Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa

Yanzun nan aka kammala kada kuri'ar zaben shugabancin majalisar dattawa ta kasa.

Sanata Godswill Akpabio ya zama sabon Shugaban zauren majalisar dattawa.

Ya samu nasarar darewa kan matsayin ne bayan doke abokin karawarsa, sanata Abdul'aziz yari daga Jihar zamfara.

Tsohon gwamnan na Akwa Ibom Kuma tsohon ministan raya yankin Naija Delta ya zama sabon Shugaban zauren majalisar dattawa na goma, bayan ya samu kuri'a 63 yayin da Sanata Abdul'aziz yari ya tashi da kuri'a 46.