On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Sanata Shekarau Ya Bukaci A Rage Yawan 'Yan Majalisar Dokoki Da Ake Dasu

SHEKARAU

Sanata Ibrahim Shekarau dake wakiltar Kano ta tsakiya, ya koka kan makudan kudin da ake kashewa da sunan tafiyar da al’amuran gwamnati, inda ya shawarci shugaba Bola Tinubu kan bukatar rage yawan ‘yan majalisar dokokin taraiyya da ake dasu.

Majalisar ta kunshi Sanatoci 109 da kuma ‘yan Majalisar Wakilai 360.

Sai dai a hirar da aka yi da sanata  Shekarau a gidan Talabijin na Channel TV ya ce a halin da ake ciki, kasar  nan bata  bukatar  zaurikan majalisun dokoki guda biyu.

Ya ce duk da kasancewar  tsarin dimukuraddiya  ya bada damar  a shigar da kowa cikin gwamnati, to sai dai  tsarin da kasar  nan ke akai, na  ‘yan majalisa  kimanin 500  na  zukewa  gwamnati makudan kudi.

Tsohon gwamnan na Kano ya kuma bada shawarar rage  yawan hukumomin da ake dasu  sakamakon yawan kudin da gwamnati ke kashewa  wajen tafiyar dasu, a maimakon yiwa jama’a aiki.