On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Sanata Yari Yasan Dalilin Gayyatarsa - Hukumar DSS

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta musanta cewa an kama Sanata Abdulaziz Yari ne saboda ya ki amsa kiran wayar shugaban kasa Bola Tinubu.

Kakakin hukumar ta DSS, Dakta Peter Afunanya, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kuma ya wallafa a shafin Twitter a ranar Lahadi, inda ya bayyana ikirarin a matsayin abin dariya da kuma rashin dacewa.

Sanarwar ta tabbatar da gayyatar Yari, inda ta ce Sanatan ya san dalilin gayyatarsa.

Har ila yau, sanarwar ta musanta zargin cewa hukumar na tuhumar alkalan kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa.

Sanarwar ta kuma musanta rahotannin da ke cewa hukumar ta DSS ta mamaye ofisoshin ICPC da hukumar 'Da'ar ma'aikata tare da kwashe wasu takardu daga hannunsu.